Amurka: Mummunan yanayi ya kashe mutum 15 a wasu jihohi

An dai yi hasashen samun guguwa mai karfi a kudancin Georgia da wani bangare na Florida

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Guguwa mai karfin gaske ta kashe mutum 15 a wasu jihohin Amuka

Yanayi marar kyau a jihohin da ke kudancin Amurka ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane a kalla 15r tare da jikkata wasu da dama.

An ayyana dokar ta baci a Georgia, inda wata guguwa mai karfin gaske ta keta wasu yankuna tare da lalata gidaje da bishiyoyi.

Bakwai daga cikin wadanda suka mutun na wajen da ake ajiye manyan motoci ne da ke kusa da iyaka da Florida.

An dai yi hasashen samun afkawar guguwa mai karfi a kudancin Georgia da kuma wasu bangare na Florida da ma Alabama.

Amurka na yawan fama da matsalar mummunan yanayi ko dai na mahaukaciyar guguwa ko na dusar kankara wadanda a mafi yawan lokuta suke janyo asarar rayua da ta dukiyoyi.