Amurka za ta sauyawa ofishin jakadancinta wuri a Isra'ila

Falasdinawa na adawa da wannan yunkuri na Amurka
Bayanan hoto,

Gwamnatin Isra'ila ta yi maraba da matakin dauke ofishin jakadancin Amurka daga Tel Aviv

Fadar gwamnatin Amurka ta ce ta na matakin farko na tattaunawa a kan dauke ofishin jakadancin kasar da ke Isra'ila daga birnin Tel Aviv zuwa birnin Kudus.

Wannan shawarar wadda ta na cikin alkawarin da Donald Trump ya yi a lokacin yakin neman zabe, za ta karya wata dadaddiyar manufa ta Amurka.

Gwamnatin Isra'ila dai ta yi maraba da wannan shiri wanda Falasdinawa suka nuna adawa da shi.

A karkashin dokokin Isra'ila, birnin Kudus shi ne babban birnin kasar, amma kuma Falasdinawa na cewa na su ne.

Shugaba Trump da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu sun yi magana ta wayar tarho a jiya Lahadi, in da suka tattauna a kan shirin kawo zaman lafiya da kuma abinda suka kira barazana daga Iran.

Mr Netanyahu ya amince da gayyatar kai ziyara Amurka a watan gobe domin tattauna yadda za a samar da matsaya guda a kan yankin gabas ta tsakiya.

Tun da farko mahukunta a Isra'ila sun amince da gina karin gidaje ga yahudawa 'yan kama wuri zauna a gabashin birnin Kudus.