Yadda sojin Nigeria suka kashe 'yan gudun hijira bisa kuskure

Alfred Davies

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Alfred Davies ya ce mutane sun shiga halin rudu

A wata hira da BBC, Alfred Davies, wani jami'in kungiyar likitocin bayar da agaji ta MSF, ya bayar da labari mai sosa rai na yadda sojojin Najeriya suka kai hari kan wani sansanin 'yan gudun hijira a kauyen Rann.

Harin dai ya hallaka a kalla mutane 90, ciki har da mata da kananan yara, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.

Sojojin Nigeria sun yarda cewar an nemi a yi hakon 'yan Boko Haram ne da harin a kauyen Rann din na karamar hukumar Kala Balge da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriyar.

Alfred Davies ya ce shi da tawagarsa na bayar da rigakafin kyanda da kuma abinci ne, a lokacin da bam na farko ya tashi a wani wurin da ke tazarar mita 300 daga inda suke.

"A lokacin muna da mutum fiye da 100 a layi .. suna jiran samun nasu kason... yara, uwaye.. kowa ya yi kasa bayan mun ji karar bam din.. Kowa ya ji tsoro sosai''.

"Kowa ya rikice, hargitsi ya tashi a ko ina," injishi, yana mai karawa da cewar, "mutane basu san ina za su je ba ko kuma me ke faruwa ba."

Asalin hoton, .

Bayanan hoto,

Alfred Davies

Misalin minti biyar bayan hakan, Mista Davies ya ce, bam na biyu ya fada wani wuri mai tazarar mita 20 daga inda suke.

Sai 'yan tawagarsa da suka fi kusa da inda bam din ya tashi suka sanar da shi ta waya cewar wadanda suka ji rauni na zuwa tantinsu domin samun kulawa.

Jami'in dan Asalin kasar Laberiya, mai kwarewa a gudanar da shiri ya ce a daidai wannan lokacin shi ya bayar da umurnin cewar 'yan tawagarsa su sauya daga raba kayan jin kai zuwa bayar da agajin gaggawa.

Ya tuna yadda mutum 20 suka kwanta a kasa cikin mawuyacin hali: cikinsu a bude, hanjinsu a kasa. Ya ce abin da ban tsoro sosai, mutanen suna ta cewa: "taimaka min, likita! Za ka taimaka min?"

"Wadanda suka raunata sun ci gaba da zuwa," in ji Mista Davies, yana mai karawa da cewar ba da jimawa ba "tantunanmu suka cika."

"Wasunsu sun mutu a tantunanmu.

"Kana cikin wani halin hargitsi- wa za ka fara bai wa kula?

Asalin hoton, MSF

Bayanan hoto,

Alfred Davies (a tsakiya ) Ya yi shekara 15 yana aiki da MSF

"Abin tashin hankali ne ka bar wanda ya ke cikin radadi kadan, ka nemi kula da wanda ya fi jin rauni, amma dole mutum ya zabi hakan," in ji shi.

"Akwai mutanen da jini ke kwarara daga jikinsu. Abinda kawai za mu iya yi a wancan lokacin shi ne mu rufe raunukansu da bandeji har sai likita ya zo''.

"E, na ga yaran da suka mutu. Na ga hanjin yaran a kasa," inji Mista Davies.

Ya ce daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, wata mata ce wadda aka yi wa riga-kafi jim kadan kafin harin.

"Mun bayar da kayan agaji ga wata mata da tagwayenta, kuma tana dariya, tana nuna mana yaranta.

"Kuma daga baya mun ga wannan matar a mace inda tagwayenta suke zauna a gefenta.. Suna kuka kuma suna taba mamansu, amma babu amsa, sun zama marayu".

"Kuma nan da nan muka fara kula da mutane. A cikin sa'a daya mun samu mutum 52," in ji Mista Davies.