Amurka ta ce za ta hada karfi da Rasha wajen yakar 'yan IS a Syria

Donald Trump ya ce a shirye ya ke su yaki 'yan IS tare da Rasha
Bayanan hoto,

Amurka da Rasha za su hada karfi wajen yaki da 'yan IS

Fadar gwamnatin Amurka ta ce shugaba Trump ya ce a shirye ya ke ya hada karfi da karfe da Rasha wajen yaki da 'yan kungiyar IS a Syria.

A taro na farko da ya yi da 'yan jarida a hukumance, mai magana da yawun fadar gwamnatin Amurkan Sean Spicer, ya ce Amurka za ta yi amfani da duk wata dama ta yaki da masu jihadin ko da Rasha ko kuma da kowacce kasa.

Tun da farko ma'aikatar tsaron Amurkan ta musanta ikirarin da ma'aikatar tsaron Rasha ta yi cewa, kasashen biyu sun kai wasu hare-haren hadin gwiwa ta sama kan 'yan IS din da ke Syria a ranar Lahadi.

Rasha ta ce Amurka ta nunawa wasu abokan kawancen kungiyar IS inda za su kai hari a kusa da garin Al-Bab.