Nigeria: Harin da sojoji suka kai Rann ya kashe 'mutum 115'

Mutum fiye da 200 ne suka mutu a harin bam din da jiragen sojoji suka kai bisa kuskure a jihar Borno da ke Najeriya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Rundunar sojin Najeriya ta nemi afuwa kan lamarin

Wani jami'in agaji ya shaida wa BBC cewa mutum 115 ne suka mutu a harin da jirgin yakin Najeriya ya kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira na Rann a jihar Borno a makon da ya gabata.

Lamarin dai ya abku ne a makon daya gabata, koda yake rundunar sojin kasar ta bayyana takaicin ta dangane da lamarin, inda ta ce tuni ta fara gudanar da cikakken bincike.

Tun da farko wani jami'i a jihar Borno, ya shaida wa BBC cewa mutum 236 ne suka mutu, kuma an yi jana'izarsu a kauyen na Rann.

Amma daga bisani shugaban karamar Hukumar ta Kala-Balge ya ce mutum 115 ne lamarin ya rutsa da su, yana mai cewa mutanen kauyen ne suka yi kuskure wurin bayyana adadin.

Baya ga 'yan gudun hijra da suka hada da mata da kananan yara da harin ya rutsa da su, akwai kuma wasu ma'aikatan agaji da suma suka rasa rayukansu.

A halin yanzu dai ana cigaba da samun bayanai game da lamarin daga jihar ta Borno da kuma irin halin da al'ummar yankin ke ciki.

A wata hira da BBC, Alfred Davies, wani jami'in kungiyar likitocin bayar da agaji ta MSF, ya bayar da labari mai sosa rai na yadda sojojin Najeriya suka kai hari kan sansanin 'yan gudun hijirar a kauyen Rann.

Alfred Davies ya ce shi da tawagarsa na bayar da rigakafin kyanda da kuma abinci ne, a lokacin da bam na farko ya tashi a wani wurin da ke da tazarar mita 300 daga inda suke.

"A lokacin muna da mutum fiye da 100 a layi... suna jiran samun nasu kason... yara, uwaye.. kowa ya yi kasa bayan mun ji karar bam din.. Kowa ya ji tsoro sosai''.

"Kowa ya rikice, hargitsi ya tashi a ko ina," in ji shi, yana mai karawa da cewar, "mutane basu san ina za su je ba ko kuma me ke faruwa ba."

Sojojin Nigeria sun yarda cewar an nemi a yi hakon 'yan Boko Haram ne da harin a kauyen Rann din na karamar hukumar Kala-Balge da ke jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriyar.