Kasashen yankin Sahel za su kara matakan tsaro

Mai masaukin baki Muhammadou Issoufou
Bayanan hoto,

Shugabannin sun ce manufar samar da dakarun hadin gwiwar shi ne, kara matakan tsaro a iyakokinsu

Shugabannin kasashen Nijar, da Burkina Faso da Mali sun amince da hada karfi da karfi dan magance matsalar tsaro a yankunansu musamman ta iyakokin su.

A wanta sanarwa ta hadin gwiwa da kasashen suka rattabawa hannu, a taron da suka yi a Yamai babban birnin jamhuriyar Nijar, sun ce yankunansu na fama da matsalar kungiyoyin 'yan ta'adda daban-daban.

Shugaba Muhammadou Issoufou mai masaukin baki, yace dakarun hadin gwiwa da za su samar za su yi aiki kwatan-kwacin wanda kawancen sojojin kasar da Najeriya, da Kamaru da Chadi su ke yi dandakilie ayyukan ta'addanci da mayakan kungiyar Boko Haram ke aiwatarwa a arewa maso gabashin Najeriya da ma makofta.