Ana kokawa kan lalacewar da hanyar Kaduna zuwa Kano ta yi

Shugaba Buhari
Bayanan hoto,

Direbobin da ke bin hanyar, sun roki gwamnatin tarayyar Najeriya ta taimaka a gyara hanyar

Masu ababen hawa da ke bin hanyar Kaduna zuwa Kano a Najeriya sun koka da asarar rayuka da dukiya da ake yi sakamakon hadurra a kan hanyar saboda lalacewarta.

Hanyar dai ita ce babbar hanyar da ta hada wasu jihohi da ke shiyyar arewa maso yammacin kasar, kuma a halin yanzu hanyar na daga cikin hanyoyin da suka fi muni a Najeriya.

Wakilin BBC wanda ya bi hanyar ta Kano zuwa Abuja, ya tattauna da wasu masu bin hanyar inda suka nuna damuwarsu kan yadda take kara lalacewa, lamarin da ya ke janyo yawaitar hadurra da asarar rayuka da dukiya.

Wasu masu motocin kansu, wadanda ba su lakanci hanyar ba da kyau, saboda lalacewarta, sun gwammace bin motar haya, saboda a cewarsu direbobin motocin haya sun fi sanin yadda hanyar ta ke da kuma kaucewa manyan ramuka saboda yawan zirga-zirgar da suke yi a kanta.