'Barazanar Trump ba ta tsorata mu ba'

Shugaba Donald Trump
Bayanan hoto,

Batun gina katanga tsakanin Amurka da Mexico, na sahun gaba a lokacin yakin neman zaben Trump

Wasu shugabannin biranen Amurka da suke bai wa baki 'yan-cirani matsuguni, sun ce ko a jikinsu, duk da barazanar Shugaba Trump na yiwuwar katse kudaden tallafin da gwamnati ke ba su.

Magajin garin birnin New York Bill de Blasio ya ce zai yaki matakin na shugaba Trump, inda ya kara da cewa ya na da cikakkiyar hujja ta fannin shari'a ta kalubalantar matakin.

Shi ma magajin garin Boston Marty Walsh, ya ce matakin tamkar don al'ummar yankinsa aka dauka, kuma idan dama ta samu zai bai wa baki 'yan-cirani matsuguni a babban zauren taron yakinsa.

Yayin da magajin garin Seattle Ed Murray ya ce babu wata barazana da za a yi masa, kuma tuni ya bai wa jami'ansa damar sake duba kasafin kudin bana dan cike gibin kudin tallafin da gwamnatin Mista Trump ta zabtare.

A nasa bangaren shugaban kasar Mexico Enrique Pena Nieto ya yi Alla-wadai da matakin shugaba Donald Trump na gina katanga a iyakar kasashen biyu.

Ya ce Mexico ba ta amince da kafa shinge ba, ya kuma yi watsi da maganar Mista Trump ta cewa Mexico ce za ta biya kudin wannan aikin.

Ya kara da cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya dace don kare hakkin baki 'yan-cirani da ke Amurka.