Manchester United ta kai wasan karshe a League Cup

Pogba

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Paul Pogba ne ya ci wa United Kwallonta

Manchester United ta samu zuwa wasan karshe na gasar cin kofin League Cup bayan ta doke Hull City 3-2 a jumullan wasanni biyun da suka fafata a matakin daf da na karshe.

United ta doke Hull City 2-0 a wasan farko, amma Hull City ta doke United 2-1 wasa na biyu da suka fafata a matakin daf da na karshe daren Alhamis, abinda ya kawo jumullan sakamakon wasannin 3-2.

Tom Huddlestone na Hull Cuty ne ya fara cin kwallo daga bugun fenareti kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Paul Pogba ya ci wa United kwallo daya bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Amma Oumar Niasse ya ci wa Hull City kwallo na biyu kimanin minti goma kafin a gama wasan.

Manchester United ta samu zuwa wasan karshe a gasar League Cup sau takwas inda ta ci gasar sau hudu. Shi kuma kociyan United din Jose Mourinho ya ci gasar sau uku.

Yanzu united din za ta hadu da Southampton a wasan karshe wadda za'a yi a watan gobe.