Barcelona ta kai matakin dab da na karshe a Copa del Rey

Barca

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Barca ta shiga jerin kungiyoyin 4 da za su fafata a wasan dab da na karshe a gasar cin kofin Copa del Rey

Barcelona ta samu zuwa wasan dab da na karshe a gasar cin kofin Copa del Rey bayan ta lallasa Real Sociedad 5-2.

Jumullar sakamakon wasanni biyun da suka buga na matakin dab da na kusa da karshe ya kasance 6-2 kenan.

Dennis Suarez ya ci wa Barcelona kwallaye biyu a minti na 17 da 82 yayin da Lionel Messi ya ci kwallo da bugun fanareti a minti na 55.

Luiz Suarez ya ci kwallo a minti 63, yayin da Arda Turan ya ci kwallo a minti na 80.

Sociedad ta samu kwallayenta biyu ne daga William Jose da Juanmi.

Barca, wadda ita ce ta ke rike da kofin ta shiga cikin jerin klob hudu wadanda za su kece reni a matakin dab da na karshe a gasar.