'Yan Yemen na tsananin bukatar abinci

Jariri mara koshin lafiya
Bayanan hoto,

Jarirai sama da miliyan biyu ne ke fama da rashin abinci mai gina jiki a kasar Yemen

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya yace karin tashin hankalin da kasar Yemen ke fuskanta, ya sanya kasar ta shiga matsanancin halin rashin abinci a duniya.

Babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da ayyukan jin kai Stephen O'Brien ya ce babu shakka kasar za ta fuskanci mummunan fari a wannan shekarar.

Ya shaida wa kwamitin cewa sama da Yamalawa miliyan 10 ne suke bukatar taimakon abinci, ana kuma bukatar taimakon cikin gaggawa domin ceto ran wadanda suka galabaita.

Ya kara da cewa jarirai miliyan biyu da rabi ne suke bukatar abinci mai gina jiki.

A bangare guda kuma Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga bangarorin da ke yaki da juna su tsagaita wuta, domin jami'an agaji su samu damar shiga kasar da ake cikin shekara ta biyu ana yaki.