Malamai da gwamnati za su yi aiki dan farfado da ilimi a Nijar

Shugaba Muhammadou Issoufou
Bayanan hoto,

Yara a Jamhuriyar Nijar ba sa samun ingantaccen ilimi

A Jamhuriyar Nijar, hukumomin kasar sun ce suna daukar matakai don magance tabarbarewar ilimi a kasar musamman ingancin sa.

Ministan ilimin firamare na kasar Dr Mamadu Dauda Marthe, ya gana da kungiyoyin malaman makaranta da na kare hakin jama'a don tattauna matsalolin da suka dabaibaye bangaren ilimi da kuma shawarwarin yadda za'a magance su.

Ministan da malam sun tattauna kan batutuwa masu muhimmanci da ke janyo tarnaki ga ilimi a kasar.

Batun rashin kishin kasa, da rashin gogewar malamai a fannin koyarwa na daga cikin matsalolin da jamhuriyar Nijar ke fuskanta ta fannin ilimi.

Harwayau, gwamnati na sanya makudan kudade a wannan fannin, amma kwalliya ba ta biyan kudin sabulu saboda yawancin daliban ba sa jin turancin Ingilishi.

A karshe masu ruwa da tsakin, sun amince a hada karfi da karfe tsakanin gwamnati, da malamai, da kungiyoyi masu zaman kan su dan shawo kan matsalar.

Wani rahoto da hukumar ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar, ya nuna yara a kasar Nijar su ne suka fi na ko'ina karancin koyar da ilimi a makarantunsu.