Yunwa na barazana ga mutum kusan miliyan 2 a Nigeria —WFP

Wata mata da 'yarta a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kungiyar likitoci ta MSF ta yi gargadi game da barazanar yunwa a yankin arewa-maso-gabashin Najeriya

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya, WFP, ta yi gragadin cewa mutum miliyan daya da dubu dari takwas na fuskantar barazanar yunwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Hukumar ta kuma ce ayyukan kungiyar Boko Haram na kafar ungulu ga yunkurin da ake yi na kai dauki ga wadanda lamarin ya shafa.

Shugabar hukumar, Ertharin Cousin, ta ce akwai wuraren da ba a iya shiga a jihar Borno, inda kungiyar ta fi karfi, saboda haka babu ma yadda za a yi a san girman matsalar bukatar abincin da suke da ita.

Babbar jami'ar ta kuma bayyana fatan cewa hukumar za ta samu kudade, duk da rahotannin da ke cewa shugaban Amurka, Donald Trump, na tunanin rage kudaden da kasar ke bai wa hukumomin Majalisar Dinkin Duniya.

A baya dai hukumomi a Najeriyar sun musanta girman matsalar, suna masu cewa hukumomin agaji na kambama ta ne kawai.

Fiye da mutane 15,000 ne suka mutu tun bayan da kungiyar Boko Haram ta fara tayar da kayan baya a shekarar 2009.