Ra'ayi: Kalubalen yaki da cin hanci a Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi: Kalubalen yaki da cin hanci a Najeriya

Kungiyar da ke sa ido kan yaki da cin hanci da rashawa a duniya ta Transparency International ta fitar da rahotonta na shekara ta 2016 kan batun yaki da cin hanci da rashawa a duniya. Kasar Denmark ce dai a sahun gaba a yakin da cin hancin. Yayinda Nigeria ke ta 136 daga cikin kasashe 176. Duk da cewa matsayin Nigeriyar ya kyautatu, in aka kwatanta da baya, wasu abubuwa da suka taso a 'yan kwanakin nan sun sa shakku a zukatan wasu kan aniyar gwamnatin ta yaki da wannan matsala. To shin ya kuke kallon yaki da cin hancin a Najeriya, shin ko wannan yaki da cin hanci na yin tasiri? Abunda muka tattauna kenan a filin na Ra'ayi Riga.