Wasu kasashen musulmai ba za su shiga Amurka ba

Yara 'yan gudun hijirar Syria
Bayanan hoto,

Mata da kananan yara da tsofaffi ne suka fi shan wahala a yakin na Syria

Shugaba Dobald Trump ya haramtawa 'yan gudun hijirar Syria shiga Amurka har sai baba-ta-gani, a wani bangare na tsaurara matakan shiga kasar musamman ga baki 'yan cirani.

Mista Trump ya ce ya dauki matakin ne domin hana 'yan ta'adda masu tsattsauran ra'ayi shiga Amurka.

An kuma dakatar da bai wa mutanen da suka fito daga kasashen Iran, da Iraqi, da Somalia, da Sudan, da Libya, da kuma Yemen izinin shiga kasar na tsahon watanni uku

Tuni magoya bayan 'yan gudun hijira suka fara sukar matakin Mista Trump, wata kungiya mai suna Civil Liberties Union mai rajin kare hakkin jama'a ta ce matakin da shugaban ya dauka cin zarafin musulmai ne, ya yin da rufewa 'yan gudun hijira kofa tamkar zai fada hannun wadanda za su cutar da Amurka.

Sanata Elizabeth Warren ta jam'iyyar Democrats ta kira matakin da wulakanta manufofin Amurka.

A bangare guda kuma matashiyar nan 'yar Pakistan, da aka bai wa lambar yabo ta Nobel Malala Yusufzai, ta ce ta kadu matuka a lokacin da ta samu labarin Shugaba Trump ya na shirin rufewa yaran da suke gujewa tashin hankali da yaki a kasashen su.

A lokacin da Mista Trump ke yakin neman zabe, ya ce ya kamata a haramtawa musulmai shiga Amurka, kuma kalaman sun janyo zazzafar muhawara a ciki da wajen kasar.