An ci zarafin bil'adam a gidajen kason Gambia

Fursunoni a kasar Gambia
Bayanan hoto,

Kungiyoyin kare hakkin bil'adam sun ce, an ci zarafin mutane da azabtar da su a lokacin mulkin Yahya Jameh na shekaru 22

'Yan sanda a kasar Senegal sun kama tsohon shugaban kurkukun kasar Gambia, Janal Bora Colley, a lokacin da yake kokarin tsalkawa kasar Guinea-Bissau.

A wata sanarwa da 'yan sandan suka fitar, sun ce an tsare shi a ranar Laraba, ka na daga bisani kuma suka mika shi ga sojojin kasar.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama dai, sun ce kusan tashe-tashen hankulan da aka yi a kasar ciki har da rikicin siyasa a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jameh, da suka hada da azabtarwa da kisan mummuke an yi su ne a gidajen kurkukun kasar Gambia.

Kasar Senegal dai ta taka muhimmiyar rawa, a daidaita rikicin siyasar da ya barke a Gambia bayan kammala zaben shugaban kasa.

Haka kuma Senegal ta taka rawa wajen lallabar Mista Jammeh barin kasar mako guda da ya wuce.

An kai ruwa rana kafin shugaba Jammeh ya amince da shan kaye a zaben da aka yi, duk da cewa da fari ya amince da shan kayen har ya kira shugaba Barrow ta wayar tarho don yi masa murna.

Mako guda bayan nan, ya kafe kan bai amince da sakamakon zaben ba, lamarin da ya sanya kasashe kawancen kungiyar ECOWAS su shiga cikin batun har dai aka sasanta ya bar kasar.