Ana bincike kan mutuwar zakuna a Afirka ta Kudu

Lion

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A 'yan watannin nan ana yawan farautar zakuna a Afirka ta Kudu

'Yan sanda a Afirka ta Kudu suna gudanar da bincike kan mutuwar wasu zakuna da yawa, wadanda ake gani, mafarauta ne suka basu guba, sannan suka yanke wasu sassa na jikinsu.

A 'yan watanni da suka gabata, an yi ta samun karuwar kashe zakuna a lardin Limpopo dake arewaci.

A lamarin na baya-bayan nan, 'yan sanda sun je wata gona inda aka gano gawarwakin wasu zakuna uku.

Biyu daga cikin zakunan, an yanke musu kawuna da dungun kafafu.

'Yan sandan sun ce suna zargin mafarautan sun ba zakunan kaji ne masu dauke da guda.

Har yanzu ba a kama kowa ba game da lamarin.