Sojoji sun sake kwato muhimmin yanki a Syria

Syria

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Rikicin Syria ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane da sa wasu gudun hijira

Rundunar sojin Syria ta ce bayan wasu makonni tana gwabza fada da 'yan tawaye, ta samu karbe iko da wani yanki wanda ke samar da ruwa ga birnin Damascus.

Kafofin yada labarai na gwamnati sun ce yanzu, tutar kasar ce ke tsaye a ma'aikatar samar da ruwan dake garin Ain al-Fijr, a yankin Wadi Barada.

Kungiyar kare hakkin mutanen Syria ta ce sojoji sun shiga yankin, a matsayin wani bangare na wata yarjejeniya wacce a karkashin ta, 'yan tawaye za su fice daga yankin ko kuma su ajiye makamansu.

Lalata bututun da ke tura ruwan da aka yi a bata kashin, ta haddasa matsanancin karancin ruwan sha a Damascus.