Hikayata 2016: Labarin 'Sarkakiya' kan yadda wani ya kusa auren kanwarsa ba tare da sani ba

Hikayata 2016: Labarin 'Sarkakiya' kan yadda wani ya kusa auren kanwarsa ba tare da sani ba

A ci gaba da karanto muku gajerun labaran da suka yi rawar-gani a gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a yau za mu kawo muku karatun labari na gaba a cikin 12 da alkalian gasar suka ce sun cancanci yabo.

A yau za mu karanto muku labarin "Sarkakiya" na Mairo Muhammad Mudi, Saida Low Cost Extension, Suleja, Jihar Neja, Najeriya.