Wata 'yar Canada ta yi kwanaki shida babu huhu

Mellisa da 'yar ta
Image caption Likitoci sun ce akan haifi mutane da irin ciwon da Mellisa ke fama da shi da ya shafi huhu

Wata mace ta shafe kwanaki shida ba tare da huhu a cikinta ba, a lokacin da take jira a yi mata dashen wani huhun.

A watan Afirilun bara ne aka yi wa Melissa Benoit, 'yar kasar Canada, tiyata kuma ita ce ta farko da aka taba yi wa irin wannan aikin a duniya.

Likitoci sun ce wani kari ya fito a cikin Melissa, kuma dole a yi mata tiyata cikin gaggawa, alhalin tana fama da matsalar cushewar numfashi.

An sanya mata huhun roba bayan an cire nata, sannan likitocin suka sake dasa mata shi bayan kwanaki shida.

Mellisa ta ce tun ta na shekara 20 ta samu wata cuta da ta shafi huhu, a hankali kuma sai ya zamo ba ta iya numfashi sosai.

Ba tare da bata lokaci ba likitoci suka ce lallai sai an mata tiyata, amma akwai hadari don ba lalle ne ta rayu ba.

''Na shafe kwanaki ba na iya numfashi sai da taimakon na'ura, sai da na yi jiran kwanaki shida kafin a samu huhun da zai dace da ni'', in ji Melissa.

Mellisa ta ce har yanzu tana ganin abin kamar almara. Ta kuma ce likitoci sun taka rawar gani don dorewar lafiyarta.

Labarai masu alaka