Za a yi mutum-mutumin gimbiya Diana

Gimbia Diana
Bayanan hoto,

Gimbiya Diana dai sun rabu da Yarima Charles kafin rasuwarta

'Ya'yan yarima mai jiran gado na Birtaniya sun sanar da shirin gina mutum-mutumin mahaifiyarsu gimbiya Diana wadda ta rasu shekara ashirin da suka gabata.

A wata sanarwa da suka fitar, yarima Williams da dan uwansa Harry, sun ce lokaci ya yi da ya kamata a san matsayin mahaifiyarsu a ciki da wajen kasar ta hanyar yin mutum-mutumin ta.

Sun kara da cewa ''Mutane da dama sun kadu matuka a lokacin da labarin rasuwar mahaifiyarmu ya karade duniya, don haka za mu yi abin da za a dade ana tunawa da ita."

Za dai a girke mutum-mutumin a fadar Kensington da ke birnin Londan wurin da marigayiyar ta rayu.

A shekarar 1997 ne gimbiya Diana ta gamu da ajalinta a wani mummunan hadarin mota.

Gimbiya Diana ta rasu a lokacin da Yarima Williams yake shekara 15, yayin da dan uwansa Harry ya ke da shekara 12.

Mai magana da yawun fadar Buckingham, ya ce sarauniya Elizabeth ta amince da matakin da jikokin nata suka dauka.