Jamus da Burtaniya sun yi Allah wadai da matakin Trump

Trump Merkel

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Angela Merkel ta ce yaki da ta'addanci da dalili ba ne na mayar da wasu abin zargi

Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi Allah wadai da matakin shugaba Trump na Amurka, na dakatar da shirin ba 'yan gudun hijira masauki, da kuma hana mutane daga wasu kasashen Musulmai bakwai shiga Amurka.

Kakakin Misis Merkel, Steffen Seibert ya ce shugabar ta gamsu cewa, yaki da ta'addanci ba dalili ba ne na mayar da wasu mutane abin zargi saboda addininsu ko asalinsu.

Sakataren harkokin wajen Burtaniya ma, Boris Johnson ya ce ba daidai ba ne a rika kyamatar wasu mutane saboda kasashen su na asali.

Magajin garin London, Sadiq Khan, wanda Musulmi ne, ya bayyana matakin na Mista Trump a matsayin abin kunya, kuma mugunta.

Matakin da Mista Trump ya dauka, ya dakatar da shirin Amurka na ba 'yan gudun hijira mafaka na tsawon kwanaki casa'in, da kuma hana 'yan gudun hijira daga Syria kwata-kwata shiga Amurka.

Kazalika, matakain ya hana 'yan kasashen Iran da Iraki da Libya da Somaliya da Sudan da Syria da kuma Yemen shiga Amurkan har na tsawon kwanaki casa'in.