An kashe sojan kundunbalan Amurka a Yemen

An American Army Apache helicopter

Asalin hoton, MOD

Bayanan hoto,

Wannan ne samane irinsa na farko da sojojin Amurkan suka kai bayan fara aikin Mista Trump

Rundunar sojin Amurka ta ce an kashe daya daga cikin sojojin kundunbalan ta sannan aka jikkata wasu uku, lokacin wani samame a shedkwatar kungiyar al-Qaeda a Yemen.

Shugaban Amurka Donald Trump ne da kansa ya bayar da umurnin kai samamen--wanda shi ne irinsa na farko tun bayan kama aikinsa.

Daya daga cikin jiragen yakin Amurka da suka kai samamen ya yi mummunan sauka, abin da ya sa aka lalata shi a wurin dake lardin al-Baida.

Sojojin Amurkan sun ce sun kashe 'yan bindiga goma sha hudu.

Majiyoyi daga Yemen sun ce adadin wadanda aka kashe din ya haura sha hudu, sannan suka ce wasu gwamman fararen hula ma sun mutu.

Masu sharhi sun ce za a iya kallon samamen a matsayin irin hobbasa da sabon shugaban ya yi na daukan tsattsauran mataki akan kungiyoyin masu da'awar jihadi.