Kungiyar tarayyar Afirka za ta fara taro a ranar Litinin

Za a zabi sabuwar shugabar kungiyar a taron bana
Bayanan hoto,

Za a zabi sabuwar shugabar kungiyar a taron bana

A ranar litinin ne shugabannin kungiyar tarayyar Afirka za su fara taron su na shekara-shakara a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha.

Daya daga cikin abin da taron na bana ya kunsa shi ne batun zabar sabuwar shugabar kungiyar wadda za ta maye gurbin Nkosazana Dlamini-Zuma.

Akwai dai mutum hudu da suke neman wannan mukami wadanda suka fito daga kasashen Botswana da Chadi da Equatorial Guinea da kuma Kenya.

Za dai a gudanar da wannan taro ne a dai-dai lokacin da wasu daga cikin kasashen kungiyar ke shirin janyewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa.

To sai dai daya daga cikin masu neman mukamin shugabar kungiyar wadda ta fito daga Kenya, Amina Mohammed ta shaida wa BBC cewa, kowacce kasa da ta kasance mamba a kotun ta na da 'yancin ficewa a duk lokacin da ta so.