An kashe sojojin Ukraine hudu tare da raunata wasu biyar

An kashe mutane dubu goma tun bayan fara rikici a Ukraine
Bayanan hoto,

An kashe mutane dubu goma tun bayan fara rikici a Ukraine

An kashe wasu sojojin kasar Ukraine hudu a wani sabon rikici da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha a gabashin kasar.

Wani mai magana da yawun sojojin ya ce an kuma raunata wasu sojojin biyar a birnin Avdiivka wanda ke iyaka da yankunan da 'yan awaren ke iko da su.

Wannan arangama ta kasance mafi muni a 'yan makonnin a gabashin Ukraine inda aka fara rikici kusan shekaru uku da suka wuce.

An dai gaza cimma yarjejeniya a rikici.

Kazalika an kiyasta cewa an kashe mutune dubu goma a rikicin.