AU: Morocco ta sake shiga cikin Tarayyar Afirka

King Mohammed

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sarki Mohammed na Morocco ya yi ta fafutuka don ganin ƙasarsa ta koma cikin Tarayyar Afirka

Tarayyar Afirka ta sake amince wa Morocco damar komawa cikin ƙungiyar a matsayin wakiliya, yayin wani taron ƙoli da shugabannin ƙasashen ƙungiyar a Addis Ababa babban birnin ƙasar Habasha.

Hukumomin ƙasar sun yi ta kamun ƙafa don samun damar shiga tarayyar, shekara 30 bayan ƙasar ta fice daga tsohuwar ƙungiyar haɗa kan Afirka wadda ta amince da yankin Western Sahara a matsayin 'yantacciyar ƙasa.

Morocco dai na ɗaukar yankin Western Sahara a matsayin wani ɓangare na ƙasarta.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Moussa Faki ya ce burinsa shi ne samun Afirka inda za a ji dusashewar harbe-harben bindiga da maye gurbinsu da kaɗe-kaɗen gargajiya da amon masana'antu

Tun da farko, gwamnatin Kenya ta taya murna ga Ministan harkokin wajen Chadi Moussa Faki Mahamat, bayan ya doke takwararsa ta Kenya, Amina Mohammed a takarar da suka yi ta shugabancin hukumar gudanarwa ta Tarayyar Afirka (AU).

Wata sanarwa da gwamnatin Kenya ta fitar ta ce "Mun yi alƙawarin aiki da shi don kare manufar ci gaban Afirka ta fuskar haɗin kai da inganta mulkin dimokradiyya da tsare kan iyakokin ƙasashe da kuma tabbatar da yalwar dukkan al'umma.

An zaɓi ministan harkokin wajen Chadi Moussa Faki a matsayin shugaban Tarayyar Afirka, inda ya gaji Nkosazana Dlamini-Zuma ta Afirka ta kudu.

Mr Faki ya fafata da ministar harkokin wajen Kenya, Amina Mohammed a zagayen ƙarshe na zaɓen da aka gudanar a taron ƙolin shugabannin ƙasashen Afirka.