Ma'aurata a Kenya sun yi aure da dala daya kacal

Wilson da Ann Mutura
Bayanan hoto,

Wilson mai shekaru 27, da amaryarsa Ann mai shekaru 24 sun sha daga bikin na su.

A Kenya, wasu ma'aurata da ke fama da talauci, sun samu yabo matuka a kafofin sada zumunta, bayan da suka kashe dala daya kacal ($1) wajen bikin aurensu, wanda suka yi da kayan da ke jikinsu a wannan hoto.

Wilson da Ann Mutura sun yi ta daga bikin nasu tun a shekara ta 2016 ne saboda sun gaza samun dala $300 (£240) da suke bukata domin bikin auren.

Ma'auratan sai suka yanke shawarar su yi aure a wannan shekarar da dan kudin da suke da shi.

Angon dai ya kashe dala daya ne kacal a kan zobba guda biyu, wanda ya nuna wa wasu mutane da suka yi ta masa tafi a yayin shagalin auren.

Sauran abubuwa da ake bukata domin gudanar da bikin kuma -ciki har da kudin samun takardar shaidar aure- cocinsu suka dauki nauyi.

Masu sharhi a kafofin sada zumunta sun yaba wa ma'auratan, inda suka yi la'akari da yadda bikin aure a kullum ke kara yin tsada.

Wannan labarin masoyan, watau Wilson mai shekaru 27, da amaryarsa Ann mai shekaru 24, dai ya ja hankalin al'ummar kasar Kenya sosai.