Isra'ila ta zargi Iran da saba doka ta hanyar gwajin makami mai linzami

An dai sanyawa Iran takunkumi a kan shirinta na makamin nukiliya
Bayanan hoto,

An dai sanyawa Iran takunkumi a kan shirinta na makamin nukiliya

Isra'ila ta zargi Iran da saba kudurin kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ta hanyar yin gwajin makami mai linzami.

Firaministan kasar Benjamin Netanyahu, ya ce gwajin makamin mai matsakaicin zango tsabagen keta dokokin majalisar dinkin duniya ne.

Mr Netanyahu ya ce zai yi kira da a sabunta takunkumin da aka kakabawa Iran din a lokacin da ya kai ziyara Amurka a watan gobe.

Jami'an Amurka sun tabbatar da gwajin makamin, amma kuma sun ce ba bu tabbas ko hakan ya sabawa kudurin majalisar dinkin duniyar wanda aka zartar a shekarar 2015, bayan an cimma yarjejeniyar takaitawa Iran din shirinta na makamain nukiliya.

Har yanzu dai Iran ba ta ce komai ba.