Canada: Ana tuhumar dan Faransa da harbi a masallacin Quebec

Alexandre Bissonnette dalibi ne dan asalin kasar Faransa

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

Alexandre Bissonnette dalibi ne dan asalin kasar Faransa

'Yan sandan kasar Canada na tuhumar wani dalibi dan asalin kasar Faransa da harbe wasu musulmai shida a lokacin da suke sallah a cikin wani masallaci da ke Quebec.

Kazalika wasu mutunen sun samu raunuka sakamakon harbe-harben bindigar inda yanzu haka mutum biyar ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

Dalibin mai suna Alexandre Bissonnette ya bayyana gaban kotu da hannu a cikin ankwa, amma bai ce komai ba.

Ana dai tuhumarsa da laifin kisan mutum shida da kuma raunata wasu.

Yanzu haka ana daukar daya mutumin dan asalin kasar Morocco da aka kama bayan kai harin Mohammed Khadir a zaman shaida.

Ana cigaba da nuna alhini a sassan kasar saboda kisa da kuma raunata mutanen da akayi.