Mutane shida da aka kashe a Masallacin Quebec

Khaled Belkacemi da Azzedine Soufiane da Aboubaker Thabti, uku daga cikin mutanen da suka rasu a harbin masallacin birnin Quebec

Asalin hoton, EVN

Bayanan hoto,

Daga hagu zuwa dama: Khaled Belkacemi da Azzedine Soufiane da Aboubaker Thabti

'Yan sanda a Canada sun kama wani mutum mai shekaru 27 da laifin harbin da aka yi a wani masallaci a birnin Quebec dake kasar, a ranar Lahadi.

Mutum Shida daga cikin masallatan da suka rasu 'yan gudun hijira ne da suka je garin domin neman mafaka da ingantacciyar rayuwa.

Khaled Belkacemi, mai shekara 60

Mista Belkacemi ya yi karatun injiniya na sinadarai a kasar sa ta asali a Algeriya, kafin ya koma Canada a shekarun 1980.

Mista Belkacemi na koyar da karatun kimiyyar abinci a jami'ar Quebec Laval, a inda ya ke auren wata Farfesa a makarantar.

Matar tasa ma tana cikin masallacin a lokacin harbin, amma ta tsira da rayuwarta.

Shugaban sashen kimiyyar abinci a jami'ar ta Laval, Jean-Claude Dufour, ya bayyana Mista Belkacemi a matsayin mutum da ya fita daban da saura, wanda ke da fara'a da kuma basira matuka, ya ce kuma yana kaunar dalibansa.

Azzedine Soufiane, mai shekara 57

An haifi Mista Suofiane a Morocco, kuma daga baya ya komo zama a Quebec shekaru 30 da suka gabata.

Yana da shagon sayar da kayan halal a cikin birnin Sainte-Foy, inda aka bayyana shi a matsayin wanda ke da muhimmanci a tsakanin al'ummar musulmin garin.

Karim Elabed, wani Limami ne da ke garin Levis da ke kusa, ya ce Mista Soufiane ya taimaka wa baki a birnin Quebec sosai Mista Elabed ya shaida wa kafofin yada labaran Canada cewa,

"Lokacin da na iso shekaru 8 da suka wuce, labarin shagonsa na fara samu, inda yawancin musulmai mazauna Quebec ke sayen kayan masarufi."

Abdelkrim Hassane, mai shekaru 41

Abdelkrim Hassane, ya yi karatun Fasahar hanyoyin sadarwa a Algeriya, kafin ya yi bulaguro. Wani abokin aikinsa ya shaida wa jaridar Globe and Mail, cewa a baya Mista Hassan ya zauna a Paris da Montreal, kafin daga bisani ya koma birnin Quebec.

Mista Hassan dai ya yi wa gwamnatin Quebec aiki a matsayin mai tsara fasahar komfuta abokin aikinshi, Abderrazak Redouane, ya ce mutum ne mai son zaman lafiya da hangen nesa.

Ya bar 'ya'ya uku.

Mamadou Tanou Barry, mai shekaru 42, da Ibrahima Barry, mai shekaru 39

Wadannan mutane biyu tashar Rediyon Canada ta bayyana cewa 'yan uwa ne, wadanda aka haifa a Guinea da ke yammacin Afirka.

An ambato su a matsayin ma'aikatan fasahar komfutoci. Mamadou Tanou Barry, mai shekara 42, na da yara biyu kuma yana yawan tura kudi a can kasar sa ta Guinea.

"Mahaifin Tanou ya rasu shekara uku da suka gabata, saboda haka sai alhakin kula da 'yanuwansa ya hau kansa. Yanzu komai ya yanke." In ji wani abokinsa a jaridar Globe and Mail.

Ibrahim dai ma'aikacin kiwon lafiya ne, wanda ke da yara hudu.

Aboubaker Thabti, mai shekaru 44

Mista Thabati Haifaffen kasar Tunisia ne, rahotanni sun ce ya koma birnin Quebec ne shekaru 10 da suka gabata, inda ya ke aiki a kamfanin bayar da magunguna.

Kanin sa ya shaida a shafin sa na Facebook cewa, yana da aure da kananan yara biyu.

Jaridar Global and Mail ta ambato wani abokinsa, Abder Dhakkar, yana cewa; "mutum ne mai kirki, wanda ke da son mutane, kuma shi ma mutane na kaunarsa."