AU ta amince da shirin rigakafi

Asalin hoton, AP
A Afirka, duk shekara cutar bakon-dauro kan yi sanadin mutuwar yara akalla 61,000
A ranar Talata ne, 31 ga watan Junairun 2017, shugabanni daga kasashen Afirka suka amince da wani kuduri na tabbatar da cewa an bai wa kowa damar samun riga-kafi a nahiyar, inda suka kafa tarihi da sanya hannu a kan wata takarda mai suna Addis Declaration on Immunization.
Takardar da shugabannin suka sanya wa hannu tana dauke da alkawarin cewa za a tabbatar duk wani dan Afirka, ko ma daga ina ya fito, zai ci moriyar riga-kafi.
An amince da wannan kudurin ne yayin taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka na 28, wanda aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Duk da cewa Afirka ta yi muhimmiyar nasara a shekaru 15 da suka gabata, wajen yin alluran riga-kafi, tsarin ya samu tsaiko, inda nahiyar ta fuskanci koma-baya wajen cimma burinta a bangaren.
Har yanzu a cikin duk yara biyar a Afirka, daya ba ya samun riga-kafi; lamarin da ya sa cututtuka da dama da za a iya magance su ke kashe yara masu dimbin yawa.
Misali, a duk shekara, cutar bakon-dauro—wacce allurar riga-kafi ke iya hana kamuwa da ita—kadai kan yi sanadin mutuwar yara akalla 61,000 a Afirka.