Miji ya yankewa matarsa kunnuwa a Afghanistan

Zarina na murmurewa a gadon asibiti
Bayanan hoto,

Zarina ta ce auren baki daya ya fita daga cikin ran ta

Wata mace mai shekaru 23 ta shaidawa BBC yadda mijinta ya daure ta, sannan ya yanke mata kunnuwa.

Lamarin ya faru ne a arewacin yankin Balkh na kasar Afghanistan.

Zarina wadda a yanzu ta ke jinya a asibitin yankin, na cikin mawuyacin hali sakamakon abinda mijin na ta ya yi ma ta.

''Babu abinda na yi wa mijin nawa, ban san dalilin da ya sa ya yi min haka ba'', inji Zarina.

Zarina ta shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar wato Pajhwok cewa, lamarin ya faru ne jim kadan bayan mijin na ta ya tashi daga bacci.

Ta kara da cewa ''Mijina mutum ne mai yawan zargi, ya kan tsitsiye ni a duk lokacin da na je gidan mu, wai na yi magana da wasu maza a hanya''.

'Yan sandan yankin sun ce sun baza komar su dan nemo mijin na ta, wanda ya tsere jim kadan bayan wannan aika-aika.

An dai yi wa Zarina aure ne ta na da shekaru 13, kuma babu wata kyakkyawar alaka tsakanin ta da maigidan na ta.

Zarina ta ce a wani lokaci da ya gabata mijin na ta ya so hana ta kai ziyara gidan iyayenta.

A karshe Zarina ta ce baki daya auren ma ya fita daga ran ta, ba ta fatan sake zama a gidan mutumin da bai san darajarta ba.

Dukan mata, da azabtar da su ba sabon abu ba ne a kasar Afghanistan, yawanci mazan matan aure na kokawa kan yadda mazajensu ke cin zarafin su ta hanyoyi da dama.

A shekarar 2015, wasu gungun mutane suka jefe wata mata har sai da ta mutu, sakamakon zargin da mijinta ya yi mata kan ta na aikata fasikanci.

Harwayau, a shekarar 2016 ma wata matashiya ta sha fama da jinya sakamakon gutsure ma ta hanci da mijinta ya yi, a yankin Ghormach da ke gundumar arewa maso gabashin yankin Faryab.

Watanni bayan nan, wata mata ta kusan rasa ranta sakamakon dukan kawo wukar da mijinta ya yi mata.