Jagoran 'yan hamayya na DR Congo ya mutu

Mr Etienne Tshisekedi

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Mista Tshisekedi fitaccen dan hamayya ne ga shugabannin kasar ta Congo tun zamanin Mobutu Sese Seko

Jagoran 'yan hamayya na Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo, Etienne Tshiekedi, ya mutu yana da shekara 84, bayan da aka kai shi Brussels a makon da ya wuce domin duba lafiyarsa.

Mista Tshisekedi, wanda ya yi fice wajen hamayya da gwamnatocin kasar tun zamanin Mobutu Sese Seko, kafin mutuwar tasa shi ne ke jagorantar yarjejeniyar sasantawa ta kasar wadda za ta kai ga nada gwamnatin rikon kwarya har zuwa lokacin saukar Shugaba Kabila a 2018.

Mutuwar Tshisekedi wani babban koma-baya ne ga yarjejeniyar zaman lafiya da Cocin Congo ta jagoranta aka yi a watan Disamba tsakanin babbar hadakar 'yan hamayya da kuma jam'iyyar Shugaba Kabila mai rinjaye.

An dai tsara tsohon dan gwagwarmayar tabbatar da Dumokuradiyyar zai jagoranci yadda za a aiwatar da wannan yarjejeniya, tare kuma da bayar da shawarar wanda yake ganin ya dace a nada Fira ministan rikon kwarya da zai jagoranci kasar har a kai ga saukar Shugaba Kabila a 2018 tare da kafa sabuwar gwamnati.

Asalin hoton, AFP/GETTY

Bayanan hoto,

Mista Tshisekedi (a tsakiya) yana da tarin magoya baya

Shi dai Etienne Tshisekedi, shi ne fitaccen dan hamayya, kuma wanda ya fi dadewa yana gwagwarmaya da gwamnati a tarihin kasar ta Congo, wanda hakan ya sa yake da magoya baya da yawa, kuma ya kan samu taron jama'a da dama a duk lokacin da ya bayyana a wani gangami.

Ya kalubalanci shugaban mulkin soji Mobutu Sese Seko, wanda ya jagoranci kasar, wadda a lokacin ake kira Zaire tsawon shekara 32, kafin Laurent Désiré Kabila, mahaifin shugaban kasar na yanzu ya ture shi a shekarar 1997.

Bayan da Joseph Kabila ya karbi shugabancin kasar a 2001, a sanadiyyar mutuwar mahaifinsa wanda daya daga cikin masu tsaron lafiyarsa ya harbe shi a ranar 16 ga watan Janairu na 2001, Tshisekedi bai tsaya a nan ba domin, ya ci gaba da zama kan gaba wajen hamayya da Shugaba Kabila wanda ya karbi ragamar shugabancin.

Yawaitar zanga-zanga da tarzoma ta addabi kasar ta Jamhuriyar Dumokuradiyyar Congo a cikin shekara ukun da ta gabata, inda 'yan hamayya suka tashi tsaye har sai Shugaba Kabila ya sauka daga mulki a karshen wa'adinsa a watan Disamba.