Mawakiya Beyonce za ta haifi tagwaye

Beyounce a hoton da ta sa a Instagram

Asalin hoton, Beyounce / Instagram

Bayanan hoto,

Beyounce na nuna cikin da take dauke da shi na tagwaye

Beyonce da mijinta Jay Z sun bayyana cewa mawakiyar za ta haifi tagwaye, kamar yadda suka rubuta a shafin Instagram, sai dai ba su ambaci lokacin da ake sa ran haihuwar ba.

Miji da matar sun rubuta a shafin Instagram din cewa, ''muna matukar godiya iyalinmu za su karu da mutum biyu, muna muku gidiya kan fatan alherin da kuke mana.''

Daman ma'auratan suna da 'ya mai suna, Blue Ivy, wadda a kwanan nan ta cika shekara biyar.

An zabi Beyonce a rukuni-rukuni har tara domin samun lambar yabo ta wake-wake ta Grammy Awards ta 2017, wanda hakan ya sa ta ci gaba da zama matar da aka fi zaba domin samun lambar a tarihi.

A watan Afrilu ake sa ran mawakiyar mai shekara 35 ta kasance jigo a wurin bikin wake-wake na Coachella, a kudancin California.

Sai dai kuma a sanarwar da suka fitar ba su bayyana ranar da ake sa ran haihuwar jariran ba.

A 2011, Beyonce ta bayyana wa masu sha'awar wakokinta ta samu juna-biyu a yayin bikin bayar da kyautar MTV Awards.

A lokacin ta fara wakarta ne ta 'Love On Top' ta hanyar sanar da masu kallo cewa tana da juna-biyu.

Kuma a karshen wakar ne, ta bude rigarta, inda ta nuna alamun cikin da ta samu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Beyonce da mijinta Jay Z sun yi aure ne a shekara ta 2008

Shi kansa mijinta Jay Z, a wakarsa ta Glory ya bayyana cewa Beyonce ta yi bari kafin haihuwar 'yarsu Blue Ivy.