DRC: Madugun 'yan adawa Tshisekedi ya rasu

Etienne Tshisekedi ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo
Fitaccen dan siyasa kuma madugun 'yan adawa a Jamhuriyyar Dimukradiyyar Congo Etienne Tshisekedi ya rasu a kasar Belgium yana da shekara tamanin da hudu a duniya.
Mukaddashin sakataren jam'iyyar UDPS ta mista Etienne, Rubens Mikindo ne ya sanar da mutuwar.
Dubban magoya bayan jagoran adawar ne suka yi dafifi a kofar gidan ɗansa Felix Etienne dan nuna alhininsu kan wannan mutuwa.
Mista Tshisekedi ya rike manyan mukamai tun bayan karbar yancin kai da kasar ta yi daga hannun Belgium a shekarar 1960, ciki har da Firai ministan kasar.
Ya taba zaman jarun na dan wani lokaci, daga bisani kuma ya bar kasar a lokacin mulkin shugaba Laurent Kabila ya kuma zama babban mai sukar gwamnatin ɗansa wato Joseph Kabila.