Murnar 'yan bautar ƙasa a Ghana ta koma ciki

Nana Akuffo-Addo
Bayanan hoto,

Kawo yanzu dai sabuwar gwamnatin Nana Akuffo-Addo ba ta ce uffan ba kan batun

Masu aikin bautar kasa a Ghana sun ci karo da wani cikas bayan an biya su alawus din Cedi 350, waton kasa da Cedi 550 da aka yi musu alkawari a baya,

Gabannin saukar tsohuwar gwamnatin Shugaba John Dramani Mahama ne, aka yi musu alkawarin karin, sai dai yanzu murna ta koma ciki.

Daliban sun ce sun sha mamaki a lokacin da suka samu kudin alawus dinsu na bautar kasa.

Yawanci dai sun ci burin yin wasu abubuwa da kudin, idan aka kara musu.

Lamarin da bai yi musu dadi ba, don haka shugabannin daliban suka ce za su gudanar da zanga-zangar lumana don nuna rashin jin dadinsu.

Suna kuma kira ga sabuwar gwamnatin shugaba Nana Akuffo-Addo, ta cika alkawarin da tsohuwar gwamnati ta dauka don bunkasa walwala da jin dadinsu.