Faransa: Anya Mista Fillon zai kai labari?

Francois Fillon
Bayanan hoto,

Francois Fillon na fuskantar matsin lamba daga jam'iyyarsa kan ya janye takarar.

A daren yau ne. ake saran gidan talabijin din kasar Faransa zai gabatar da tsohuwar tattaunawar da ya yi da matar dan takarar shugabancin kasar Francois Fillon shekaru goma da suka gabata.

A cikin tattaunawar dai Mista Fillon ya musanta cewa matarsa ta taba aiki a matsayin mataimakiyarsa a majalisar kasar.

Wakiliyar BBC ta ce watakila burin mista Fillon na zama shugaban Faransa ka iya dusashewa cikin kankanin lokaci.

Ana dai binciken Fillon, kan zargin cewa ya biya matarsa albashi a matsayin mai taimaka masa kan aikin majalisa alhalin ba ta yi aikin ba.

Sai dai dukkan mutanen biyu sun musanta wannan zargi.

Kafin fitowar wannan maganar, Mista Fillon yana da farin jini a jam'iyyarsa, kuma ana ganin shi ne zai kada jam'iyyar center right Republican mai ra'ayin mazan jiya, amma a yanzu yawancin 'yan jam'iyyarsa na kiran ya janye daga takara.