Nigeria: Kotu ta ɗaure wani soja shekara 7 a gidan yari

Wata kotun sojin Najeriya a Abuja

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Wata kotun soji kenan yayin zamanta a Abuja

Kotun musamman ta rundunar sojin Najeriya da ke zamanta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta yanke wa wani sojan kasar zaman gida yari na shekara bakwai, bayan samunsa da laifin kisa ba da niyya ba.

Sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, kotun ta musamman ta same shi ne da laifin harbe wani mutum, mai suna Umar Alkali a kasuwar Monday Market da ke Maiduguri, a ranar 23 ga watan Disamba na shekara ta 2015.

Kotun ta ki amincewa da hujjar da sojan ya gabatar ta cewa ya harbi mutumin ne a kokarin kare kansa.

Inda ya ce mutumin ya yi kokarin kwace bindigarsa ne, wanda a kan haka ne shi kuma ya harbe mutumin.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Birgediya Janar Sani Usman Kuka-sheka ya bayar mai dauke da bayanin, ta kuma ce kotun, wadda ke karkashin shugabancin Birgediya Janar Olusegun Adeniyi, ta sami wani sojan da laifin guje wa aikin soji, wanda ta yanke masa hukuncin daurin wata 14.