Golan Masar El Hadary ya fitar da ita kunya

AFCON

Asalin hoton, GABRIEL BOUYS

Bayanan hoto,

Gwarzon golan Masar da ya ture bugun fanareti guda biyu

Masar ta doke Burkina Faso da ci 4-3 a bugun fanareti bayan sun tashi canjaras 1-1 inda ta tsallaka zuwa zagayen ƙarshe a gasar cin kofin Afirka a karo na tara.

Daɗaɗɗen golan Masar Essam El Hadary ne ya fitar da ƙasarsa kunya, inda ya tare bugun Bertrand Traore, Masar ta samu nasara.

Yayin fafata wasan, Mohamed Salah ne ya fara ciyo wa Masar ƙwallo bayan ya maka wani ƙayataccen ƙwallo saman ƙuryar hagu cikin ragar Burkina Faso.

Sai dai Burkina Faso ta farke lokacin da Aristide Bance ya ajiye ƙwallon da Charles Kabore ya bugo masa a ƙirji sannan ya tamfatsa ta a raga.

Burkina Faso ce ƙasar farko da ta ci Masar ƙwallo a wannan gasa ta cin kofin Afirka.

Asalin hoton, Gabriel Bouts

Bayanan hoto,

'Yan wasan Masar suna rarrashin golan Burkina Faso Herve Koffi

Golan Burkina Faso Herve Koffi ɗan shekara 20, ya yi wani tsalle ya ture ƙwallon Abdallah El Said yayin bugun fanareti.

Sai dai, bai zo da sa'ar takwaransa El Hadary ba - ɗan wasa mafi tsufa a tarihin gasar cin kofin Afirka, wanda a yanzu yake da damar cin kofin Afirka na biyar a rayuwarsa.