Minista ya ajiye aiki kan sassauta hukuncin rashawa

Romania

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Masu zanga-zanga sun yi dandazo a gaban ginin ofisoshin gwamnati da ke birnin Bucharest

Ministan ciniki a ƙasar Romaniya ya sauka daga muƙaminsa saboda taƙaddama a kan dokar kankare laifi ga wasu nau'o'in cin hanci.

Hakan dai ya haddasa gagarumar zanga-zanga mafi girma a Romania tun bayan faɗuwar tsarin kwamunisanci a shekarar 1989.

Florin Jianu ya ce gwamnati ta kunyata magoya bayanta don haka shi ba zai iya ci gaba da riƙe muƙaminsa na minista ba.

A ranar Laraba, mutum 250,000 ne suka fantsama kan tituna don bayyana adawarsu da wannan doka.

Dokar wadda ba ta majalisa ba ce, ta yi tanadin cewa ba za a ɗaure jami'an gwamnati ba matuƙar laifin da suka aikata bai wuce darajar dala dubu 48 kwatankwacin Naira miliyan 20 ba.

Wasu ƙasashe ciki har da Jamus da Faransa da Amurka sun gargadi Romania kan ɓata sunanta a idon duniya da kuma hulɗarta da Tarayyar Turai da ƙungiyar tsaro ta NATO.