Crouch ya shiga jerin masu ƙwallo 100 a ragar Premier

EPL

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

A kakar da Crouch ya yi da Southamton ya ci ƙwallo 12

Peter Crouch ya ce shiga jerin hamshaƙan 'yan wasa 26 da suka ci ƙwallo 100 a gasar Premier ya sanya masa "shauƙi".

Ɗan wasan gaba na Stoke ɗin ya kafa wannan abin tarihi ne lokacin da ƙungiyarsa ta yi kunnen doki da Everton ranar Laraba, shekara 15 bayan cin ƙwallonsa ta farko a wata babbar ƙungiyar Ingila.

Crouch mai shekara 36 ya ce, "Akwai gwanayen 'yan wasa a jerin masu ƙwallo 100, don haka shiga sahunsu wani ƙasaitaccen abu ne a wajena.

"Ƙwallon tana shiga raga, sai na ji wani irin daɗi ya lulluɓe ni."

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Mafi yawan ƙwallayen da Crouch ya yi da kai ya buga su

Ƙwallon tarihin ya zo ne lokacin da Crouch ya ɗan zungura ta cikin raga a farkon rabin lokaci yayin karawa da Everton, inda ta kai shi jerin hamshaƙan 'yan ƙwallo irinsu Alan Shearer da Thierry Henry da Ian Wright da Robbie Fowler.

Tsohon ɗan ƙwallon Ingilar wanda ya buga wasa 419 a gasar Premier ya ce, "Abin burgewa ne mutum ya samu kansa a wannan jeri don kuwa akwai ɗumbin 'yan wasan da nake ganin ƙimarsu."

"Wasu ƙwallayen da na ci a suna da ƙayatarwa, wasu kuwa ba yabo ba fallasa, amma dai duk sun yi min rana." Inji shi.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Daga 2009 zuwa 2012, Couch ya ci ƙwallo 12 a Tottenham

Kocin Stoke City Mark Hughes ya taya gogaggen ɗan wasan gaban murna, wanda ya kutsa kansa cikin rukunin 'yan wasan da kulob ɗin ke damawa da su a kakar bana, bayan mayar da shi gefe a akasarin wasannin bara.

Hughes ya ce, "Abu ne mai ƙayatarwa. Nasara ce a gare shi. Tun da ya zo cikinmu, ya yi zarra."

Ƙwallon da Crouch ya ci ta farko a gasar Premier ita ce wadda ya ci a Newcastle a watan Afrilun 2002.

Bayan shekara 15 ya yi murnar cin ƙwallonsa ta 100 da rawar nan da ya fara yi kafin zuwa gasar cin kofin duniya a 2006.

Asalin hoton, Rex Features

Bayanan hoto,

Crouch na da ƙwallo 22 a Liverpool