An gano gawar matashi rataye jikin bishiya a Kano

Nigeria
Bayanan hoto,

A watan jiya ma an samu gawar wata tsohuwa rataye a jikin bishiya a dai wannan gari na Gezawa da ke cikin jihar Kano

Ana zargin wani matashi mai kimanin shekara 30 ya rataye kansa a ƙaramar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Da safiyar Alhamis ne aka wayi gari da ganin gawar matashin rataye a jikin wata bishiya a ƙauyen Tsamiya Babba.

Rundunar 'yan sandan Kano ta ce bisa dukkan alamu matashin ne ya rataya kansa.

Sai da matashin ya cire tufafinsa tsaf sannan ya rubuta "Nura", kuma ya ajiye tufafi da carbi da takalmansa a ƙasan bishiyar da ya rataye kansa.

Mutanen ƙauyen Tsamiya Babba sun ce matashin baƙo ne, don kuwa babu wanda ya san shi ko a ƙauyukan yankin masu maƙwabtaka.

Ya zuwa yanzu ba a san daga inda matashin ya fito ba, kuma ba a san dalilin da ya sanya shi kashe kansa ba.

Ko a watan jiya ma an samu wata tsohuwa rataye a jikin bishiya cikin ƙaramar hukumar Gezawa, 'yan sanda sun ce suna gudanar da bincike a kan kisan tsohuwar, wadda suka ce suna kyautata tsammanin ba kashe kanta ta yi ba.

Mai magana da yawun 'yan sanda a Kano, DSP Magaji Musa Majia, ya ce sun ƙaddamar da bincike a kan ratayar matashin.