Netanyahu: Za mu gina wa yahudawa gidaje 6,000

Benyamin Netanyahu
Bayanan hoto,

Mista Netanyahu ya ce har yanzu yahudawa na cike da bakin cikin raba su da gidajensu da kuma dukiya, dan haka gwamnatinsa za ta share musu hawaye

Fadar White House ta sanar da cewa gwamnatin shugaba Trump ba ta dauki matsaya a hukumance ba, kan mamayar matsugunan Falasdinawa da Isaraela ta yi ba.

Sai dai sake gina wasu matsugunan da fadada yankin da Israela za ta yi iko da shi, zai kawo nakasu a kokarin zaman lafiyar da ake son ya tabbata a yankin.

Wannan sanarwar ta zo ne sa'a guda bayan Firai ministan Israela Benyamin Netanyahu ya yi alkawarin gwamnatinsa za ta bada izinin sake ginawa yahudawa wasu gidaje a yankin Falasdinawa bayan an dakatar da ginin yankin Amona.

Sai dai Netanyahun bai yi bayanin lokaci ko wurin da za a yi ginin ba, idan har ta tabbata wannan shi zai kawo gina matsuguni mafi girma da gwamnatin Israela ta yi cikin shekaru ashirin.

Netanyahu ya kara da cewa Yahudawa na cike da bakin cikin yadda aka tilastawa 'yan uwansu barin gidajensu, da dukiyarsu.

Wannan dalili ya sanya gwamnatinsa za ta gina mu su sabbin gidaje dubu shida, kuma tuni an sanya 'yan kwamiti duba wurin da ya dace da aikin da kuma lokacin fara shi.