Amurka ta kakaba wa Iran takunkumi bayan gwajin makami mai linzami

Iran ta yi gwajin makami mai linzami

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Amurka ta kakaba wa Iran takunkumi bayan gwajin makami mai linzami

Amurka ta kakaba wa Iran wasu sabbin jerin takunkumi domin ladabtar da ita akan gwajin makami mai linzamin da ta yi kwanan nan, wanda gwamnatin ta ce tamkar Iran tana goyon bayan ta'addanci ne.

Matakin da Amurka ta dauka dai ya shafi kamfanonin 12 ne, da kuma wasu mutane 13 'yan kasar Iran da kuma wasu kasashe daban.

Kakakin fadar gwamnatin Amurka ta White House, Sean Spicer, ya ce matakin na nuni da cewa yarjejeniyar kasa-da-kasa kan shirin nukiliyar Iran ya saba da muradun Amurka.

Sai dai a wata ziyarar da ya kai birnin New York, ministan harkokin wajen Jamus, Sigmar Gabriel, ya ce Iran ta yi karen tsaye ga kudirin Majalisar Dinkin Duniya, amma wannan bai shafi yarjejeniyar ba.

Iran dai ta ce takunkumin da aka kakaba mata ta keta dokokin yarjejeniya da aka kulla da Majalisar Dinkin Duniya, a inda aka ta amince da cewa za ta sassauta shirin samar da makaman nukiliya a kasarta.

Kasar ta kuma kara da cewa za ta mayar da martani ta hanyar sanya dokokin takaitawa kamfanonin Amurka da ta ce na hulda da wasu kungiyoyin ta'adda a yankin.