Kotu ta bayar da belin dan bala Mohammed kan naira 100m

Shamsudeen

Asalin hoton, EFCC

Bayanan hoto,

Hukumar EFCC na kuma zargin Shamsuddeen Bala Mohammed da hallata kudin haram

Wata babbar kotu a Najeriya ta ba da belin Samshuddeen Bala, dan tsohon ministan birnin Abuja, Sanata Bala Muhammad, wanda ake tuhuma da zambar naira biliyan 1.2.

Mai shari'a Nnamdi Dimgba da ke sauraron karar ya ba da belin shamsuddeen kan kudi naira miliyan dari da kuma gabatar da mutane biyu masu tsaya masa wadanda dole su kansance manyan 'yan kasuwa ko ma'aikatan gwamnati.

Haka kuma dole ne masu tsaya masan su kasance sun mallaki gidaje a Abuja ko Lagos.

Kuma kotun ta ce dole dan ministan ya gabatar da shaidan biyan haraji na shekara shidan da ya gabata kuma kada ya yi tafiya ba tare da izinin kotun ba.

Dan tsohon ministan dai ya musanta zargin aikata laifuka 15 da hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta EFCC ta yi masa.

A ranar daya ga watan Fabrairu ne EFCC ta gurfanar da Shamsuddeen tare da kamfanoni hudu wadanda suka hada da Bird Trust Agro Allied Limited da Intertrans Global Logistic Limited da Diakin Telecommunications Limited da kuma Bal-Vac Mining Nigeria Limited.