Dan Masar ne ya kai harin gidan kayan tarihi a Faransa

An tsaurara matakan tsaro a asibitin da aka kwantar da maharin
Jami'ai a kasar Faransa, sun ce mutumin da ake zargi da kai wa sojojin kasar hari a wajen gidan adana kayan tarihi na Louvre a birnin Paris dan asalin kasar Masar ne.
Mutumin mai shekaru 29, ya yi rayuwarsa a kasar Dubai, a yanzu haka kuma ya na cikin mawuyacin hali a asibitin cikin matakan tsaro.
Mai shigar da kara na gwamnatin Faransa, ya ce maharin ya far wa sojojin ne dauke da adduna a hannunsa, wadanda suke gadin kofar shiga wani babban shago da ke gefen gidan adana kayan tarihin.
Tun da fari shugaba Francois Hollande, ya yaba da karfin hali da jajircewar sojojin da suka harbi mahari.
Mista Hollande ya ce sojojin sun hana aukuwar harin ta'addanci, kuma hakan abin a yaba musu ne.
Ya kara da jinjina irin martanin da sojojin suka mayar, kuma wannan ya nuna ingancin aikin Operation Sentinielle na kare Faransa daga farmaki.
Kafofin watsa labaran Faransa sun ruwaito cewar sojojin sun harbi maharin har sau uku, tare da dukan shi a ciki.