EU: Za mu hada kai da Libya dan magance matsalar 'yan cirani

'Yan cirani a kwale-kwale
Bayanan hoto,

Dubban mutane ne ke mutuwa ya yin ketara tekun Bahar Rum, dan isa nahiyar turai.

Kasashen kungiyar tarayyar turai sun cimma matsaya kan matakan da za su dauka da hadin gwiwar gwamnatin Libya dan magance kwararar baki 'yan cirani.

Mai masaukin baki Firai ministan Malta Joseph Muscat, ya ce an cimma wata yarjejeniya da kabilun buzaye da ke kudancin kasar Libya.

Wanda masu fasa kwaurin mutanen ke bai wa sama da dala miliyan shida a kowanne mako, idan za su wuce da 'yan cirani.

Mista Muscat bai yi karin haske kan yadda shirin na hadin gwiwa zai kasance ba, amma kwararru a kasar Libya sun ce za su nemi cikakken hadin kan Buzayen dan samun nasarar wannan aiki.

'Yan ci rani daga sassa daban-daban na duniya, musamman kasashen da ake yaki irin gabas ta tsakiya, su ke kokarin ketare tekun Bahar Rum dan isa nahiyar turai.

Shi ma mai magana da yawun hukumar da ke sa ido kan masu kaura ta Majalisar Dinkin Duniya Leonard Doyle, ya ce sun yi maraba da wannan mataki.

Kuma hakan zai sanyayawa 'yan ciranin gwiwar yin tafiyar kasada, da neman mafaka a wasu kasashe.

Ya yin da za a shawo kan 'yan ciranin da wasu kasashe suka ki ba su mafaka, su koma gida.