Yara 'yan gudun hijirar Syria ba sa zuwa makaranta

Yara 'yan Syria
Bayanan hoto,

Mata da yara kanana da kuma tsofaffi ne, suka fi shan wahala a yakin na Syria

Kusan rabin yara 'yan kasar Syria da sukai gudun hijira saboda yakin basasar da kasar ke ciki ba su ke zaune ba tare da zuwa makaranta ba.

Dukkuwa da cewa shugabannin kasashen duniya da sukai wani taro a bara, sun yi kiran ya kamata yaran nan su samu ingantaccen ilimi.

Wannan kira dai an yi shi ne a taron da aka yi dan neman tallafin fiye da dala biliyan goma sha biyu, dan tallafawa 'yan Syria da yakin ya shafa.

An dai samu kusan kashi tamanin cikin dari na kudaden, amma kuma wasu matsalolin sun hana yaran zuwa makaranta.

Wasu daga cikin su dai kan yi ayyukan karfi dan samun abin rufin asiri, ya yin da ake yi wa matan su aure, ya yin da a wasu lokutan kuma makarantun sun yi nisa da wuraren da suke zaune.

Shekaru biyar kenan da fara yakin basasar Syria, tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a bangare guda kuma da masu tada kayar baya na kungiyar IS.

Dubban 'yan Syria ne suka rasa rayukansu, wasu dubban kuma suka rasa muhallansu, ya yin da miliyoyi sukai gudun hijira kasashe makofta.