Nigeria: Mutane dubu 250 ke kamuwa da kansa a shekara

Kwayar cutar Kansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Cutar Kansa na hallaka mutane da dama a duniya

Ciwon Daji ko Cancer a turance, cuta ce wadda masu fama da ita ke mutukar kokawa, ba wai kawai yadda ta ke cin tsokar jiki ba, harma da yawan cacar kudi wajen neman magani.

A Najeriya, ƙarancin kayan aikin kula da masu cutar kan jefa ɗimbin marasa lafiya cikin mawuyacin hali, a wasu lokuta ma lamarin kan kai su ga mutuwa.

Wasu bayanai dai sun ce 'yan Nijeriya kimanin dubu 250 ne ke kamuwa da cutar ta kansa a duk shekara.

Wata mai fama da cutar a asibitin Abuja a babban birnin Najeriya, ta koka da rashin kayan aiki da sashen kula da masu cutar ke fama da ita.

Abun da take gani ya na daya daga cikin matsalolin da al'umma ke fuskanta wajen neman waraka daga cutar.

Bayanai sun nuna cewa na'urar gashi guda 7 ake da ita a Najeriya maimakon 300 da hukumar kiwon lafiya ta duniya ta ce ana bukata.

Matukar tsadar kudin magani da rashin samun tallafi na kara tsunduma masu dauke da cutar cikin wahala.

Nau'in cutar da aka fi fama da ita a kasar sun hada da Kansar mama, da ta mahaifa wadda mata ke matukar shan wahala akan ta.

An yi kira ga gwamnatoci su taimaka, wajen bai wa m,asu cutar magani kyauta saboda tsadar shi.