Wasu matasan Ibo sun fi son Turanci akan harshensu

Nigeria Igbo

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wasu masu rike da sarautun gargajiya na al'ummar Ibo a Najeriya

A Najeriya, matasa da dama na al'ummar Ibo sun gwammace su yi amfani da harshen Turanci ko ma Turancin burokin, a maimakon harshensu na asali, wato Ibo.

Hakan kuwa yana haifar da daukushewar harshen na Ibo, har ma ana fargabar al'amarin na iya kai harshen ga bacewa baki dayansa, idan ba a dau aniya ba.

Kuma mutane da dama, ciki har da masana a fannin harsuna, suna zargin iyaye da zama ummul-habaisin aukuwar hakan.

Farfesa Benson Ogwuegbu, wani masani a fannin harshen Ibo ya ce, hakika harshen Ibo yana fama da matsalar dakushewa, sakamakon yadda iyaye suka gwamnace yin amfani da harshen Turanci bisa na Ibo, kuma ba sa yin amfani da shi a gidajensu.

Don haka ya ce akwai bukatar a sauya wannan hali.

Mista Chris Aneke, wani mahaifin yara biyar, ya ce, haka maganar take, saboda iyaye da yawa suna ganin koyar da yara harshen Ibo zai hana su nakaltar Turanci.

Sun ture fa'idojin sanin harshen uwa. Amma ya ce shi kam yana koyar da nasa yaran harshen Ibo.

Sai dai Dokta Okeke Chukuwuma, wani masani na harshen Ibo, ya ce sun tashi tsaye don shawo kan wannan matsala.

Ya ce, suna ta kokarin ganin harshen ya ci gaba da rayuwa, tare da bunkasa. Kuma suna kokarin ganin 'yan boko su ma sun taimaka ta wannan fuska.